Ana ci gaba luguden wuta Aden

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gwamnati na kokarin fatattakar 'yan Houthi

Mayakan sa kai da kasar Saudiya ke marawa baya na ci gaba da kai hare-hare kan 'yan tawaye na kabilar Houthi da ke kudancin birnin Aden.

Nasarar da suka samu tun ranar Litinin ta sanya gwamnatin kasar Yemen da ke gudun hijira ayyana cewa an fatattakin 'yan tawayen Houthin daga birnin.

Mataimakin shugaban kasar Khaled Bahah, ya wallafa a shafin sa na Facebook cewa sun karbe aden daga 'yan tawayen.

A wata tattauna da gidan talabijin din kasar, da ba sa fai ya ke yi ba, shugaba AbdulRabbuh Mansour Hadi wanda ke gudun hijira a kasar Saudiyya yace nasarar da aka samu a birnin Aden somin tabi ne da ke nuna an kusan karbo shi.

An ci gaba da luguden wuta ta sama a babban birnin kasar Sanaa, wanda kasar Saudiyya ke jagoranta da nufin karya lagon 'yan tawayen Houthi.