Iraqi - An cafke wasu kan zargin kai harin bam

Dakarun kasar Iraqi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dakarun kasar Iraqi

Mahukunta a kasar Iraqi sun ce sun cafke wasu da ake zargi da hannu wajen kai harin bam a wata kasuwa, inda mutane 120 suka hallaka.

Ministan harkokin cikin gida na kasar Iraqi ya ce an cafke mutane 5 da ke da hannun a harin na ranar Jumma'a, kuma zasu fuskanci shari'a.

Kungiyar I-S ta masu da'awar jihadi ta ce ita ke da alhakin kai harin a ranar Jumma'a a gabashin garin Khan Bani Saad dake lardin Diyala.

Bam din ya fashe ne a daidai lokacin da kasuwar ta cika ta batse da masu sayayya don bukukuwan karamar sallah, bayan kammala azumin watan Ramadan.