Bai kamata jami'an SSS su shiga gidana ba — Dasuki

Image caption Mai alfarma, Tsohon sarkin musulmin Nigeria, Alhaji Ibrahim Dasuki

Mahaifin tsohon mai ba wa tsohon shugaban Najeriya shawara kan tsaro, mai alfarma tsohon Sarkin Musulmi na 18 a Nigeria, Alhaji Ibrahim Dasuki, ya nuna rashin jin dadinsa a kan yadda jami'an tsaro suka shiga gidansa na Sokoto inda suka yi binciken kwakwaf.

Dasuki ya ce bai kamata jami'an tsaro su shiga gidansa ba tare da neman izininsa ba, saboda akwai bambamci tsakaninsa da dansa Kanar Sambo Dasuki da gidansa.

Ya kara da cewa ya kamata jami'an tsaro su nemi izinin shiga gidansa, ba wai kai-tsaye su shiga ba tare da neman izini ba.

Jami'an hukumar farin kaya ta SSS dai sun kai samame gidan Kanal Sambo Dasuki a Abuja da kuma gidan mahaifin nasa, Alhaji Ibrahim Dasuki, a Sakkwato, ranar Juma'a.