Boko Haram ta kai hari a Kamouna

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rahotanni sun ce yara tara ne suka mutu a garin.

Rahotanni daga garin Kamouna na cewa mutanen da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kai hari inda suka kone kusan garin baki daya.

Rahotannin na cewa yara tara ne suka hallaka sakamakon konewar da suka yi da wutar da ta tashi a garin.

Wakilin BBC a kamaru ya ce sauran jama'ar garin kuma sun tsere zuwa garuruwan da ke makwabtaka da garin.

Kungiyar ta Boko Haram dai ta zafafa wajen kai hare-hare a Kamaru, koda yake gwamnatin kasar ta sha alwashin murkushe kungiyar.