Buhari yana ganawa da Obama

Hakkin mallakar hoto mark knoller
Image caption Shugabannin biyu suna son hada gwiwa domin yaki da Boko Haram.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, yana can yana ganawa da Shugaba Barack Obama a fadar White House.

Jami'an fadar White House sun ce shugabannin biyu na tattaunawa a kan yadda za su hada kai domin yaki da kungiyar Boko Haram.

Dangantaka tsakanin Amurka da Najeriya ta yi tsami a lokacin shugabancin Goodluck Jonathan bisa zargin da ake yi wa sojin Najeriya na taka hakkin dan adam.

Shugaba Buhari ya sha alwashin kawar da matsalar cin hanci, kana ya dauki aniyar kwato kudaden da aka sace daga Najeriya aka boye a bankunan Amurka da Switzerland da sauran kasashen waje.