An bude bankuna a Girka

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Mutane a layukan cirar kudi

An samu dogayen layuka a wasu daga cikin bankunan kasar Girka bayan da suka dawo bakin aiki sakamakon rufewar da akayi na kusan makonni uku.

Bankunan sun bude ne bayan da majalisar dokokin kasar ta zartar da kudurin tsuke bakin aljihu a makon daya gabata a wani bangare na ceton kasar daga halin da ta shiga.

Akwai wasu abubuwa da suma aka dakatar da su atsarin tafiyar da bankin.

Daga cikin abubuwan ba za a iya cire kudi ba, sannan an rufe hanyoyin aikewa da kudi zuwa kasashen waj.

Akwai kuma ka'ida a wajen cire kudade inda a maimakon a rinka cire kudi kullum yanzu an takaita kana an kuma kara kudaden haraji.

A jiya lahadi shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya ce Matsalar Girka ta nuna cewa akwai bukatar gyara a tsarin gwamnatocin kasashen da ke amfani da kudin bai daya na yuro musamman ta fuskar kasafin kudin .