An fitar da Hissene Habré daga kotu

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ana zargin Hissene Habré da aikata laifukan yaki.

An fitar da tsohon shugaban Chadi Hissene Habre daga cikin kotun da ake yi masa shari'a kan aikata laifukan yaki.

Ma'aikatan kotun sun fitar da shi ne bayan da ya rika ihu, yana cewa shari'ar "shirme" ne kawai.

Tsohon shugaban kasar Chadi, Hissene Habré, ya isa wata kotun kasar Senegal da safiyar ranar Litinin.

Ana zargin Mr Habré da bayar da umarnin kisan dubbana mutane da azabtar da su a lokacin da yake mulki.

An kori wasu daga cikin masu goyon bayansa daga kotu saboda sun tayar da hargitsi.

Mr Habré ya tsere zuwa Senegal daga Chadi shekaru 25 da suka wuce.

Shari'ar da ake yi masa -- wacce kungiyar kasashen Afirka ta shirya --- ita ce ta farko da ake yi wa wani tsohon shugaba a wata kasar da ba tasa ba.