Jirage marassa matuka sun kawo cikas ga ayyukan kashe gobara a Amurka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gobarar daji

Masu kashe gobara a Amurka sun soki lamirin masu jirage marasa matuka wadanda suke yawo da jiragen a kusa da dajin da ke cin wuta wanda hakan ya dakatar da jirage masu saukar ungulu daga kokarin da suke na kashe gobarar.

Jami'an hukumar kashe gobarar sun ce mutane sun shiga tsaka mai wuya saboda jirage masu saukar ungulu sun kasa tashi.

Jirage masu saukar ungulu na taimaka wa wajen kashe gobarar daji a San Bernadino-County a karshen makon daya gabata.

Ana kyautata tsammanin Jirage marasa matuka biyar da suka yi shawagi akan wutar na daukar hotunan bidiyo ne ga wadanda suka mallake su.

Hotunan da aka nuna a labarai sun nuna yadda mutane suka bar motocinsu domin tsira daga gobarar wadda ta mamaye wata babbar hanya da ta hada Los Angeles da kuma Las Vegas.

Wutar dai ta kona ababan hawa 20 tare da lalata wasu goma.

Tuni dai hukumar dake kula da dazuka ta Amurka ta yi gargadin akan daina yawo da jirage marasa matuka a kusa da wuta.

Gobarar dai ta lalata kadada fiye da 4,250.