Bam ya kashe mutane da dama a Turkiyya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Bam din ya tarwatse ne a wata cibiyar raya al'adu.

Wani abu da ya yi bindiga ya halaka akalla mutane 28 a garin Suruk da ke kudu-maso-gabashin Turkiyya, wanda kuma ke iyaka da kasar Syria.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Turkiyya ta ce mutane kusan 100 kuma sun jikkata.

Wasu hotuna da aka yada a kafafen sada zumunta sun nuna gawawwaki da kuma wadanda suka ji rauni kwance jina-jina.

Abun dai ya tarwatse ne a wata cibiyar raya al'adu, inda daruruwan Turkawa da Kurdawa matasa ke tattaunawa a kan yadda za a sake gina garin Kobani na kasar Syria da ke iyaka da Turkiyar.

Wasu rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun ce wani dan-kunar-bakin-wake ne ya kai harin da niyyar ramuwar gayya game da kwace iko da Kobani da Kurdawa suka yi.