An damke dillalin makamai na Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Nigeria sun ce za su kawar da Boko Haram

Rahotanni daga Nigeria sun ce sojojin rundunar hadin-gwiwa ta kasa-da-kasa sun damke wani babban dillalin makamai na kungiyar Boko Haram.

Wata majiyar tsaro ta tabbatar wa BBC cewa, sojojin Nigeria tare da hadin gwiwar na Chadi sun kama, Babagana Gwange a cikin yankin kasar Chadi a ranar Talata.

Bayanai na nuna cewar Babagana Gwange shi ne babban mai yi wa kungiyar Boko Haram safarar makamai.

An dade ana kokarin gano inda 'yan Boko Haram ke samun manyan makamai da suke kai hare-hare a kan fararen hula.

Kasashen Nigeria, da Nijar, da Kamaru, da Chadi, da kuma Benin sun kafa rundunar kawance domin ganin an kawo karshen ayyukan Boko Haram da ya jefa miliyoyin mutane cikin mawuyacin hali.

A karshen wannan watan ne rundunar za ta soma aiki domin fatattakar 'yan Boko Haram.

Hakkin mallakar hoto Nigeria Govt
Image caption Manyan jami'an tsaro a Nigeria