An dage shari'ar Habré zuwa Satumba

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mr Habre ya ki gabatar da lauyoyin da za su kare shi.

Wata kotu a Senegal ta dage shari'ar da take yi wa tsohon shugaban kasar Chadi, Hissene Habre, bisa zargin aikata laifukan yaki.

Tsohon shugaban kasar ta Chadi, Hissene Habré, ya gurfana a gaban kotun ne a kwana na biyu a jere.

Alkalin kotun ya bayar da umarnin dakatar da shari'ar zuwa watan Satumba har sai an samu lauyoyin da za su kare Mr Habré.

Mr Habré ya ki gabatar da lauyoyin da za su kare shi saboda bai amince da kotun ba.

Ana zargin sa ne da kashe dubban mutane da musguna musu a lokacin da yake shugabancin Chadi.

Wannan shi ne karon farko da ake gurfanar da shugaban wata kasa a nahiyar Afirka, a kasar da ba tasa ba.