Shugaban kamfanin Toshiba ya yi murabus

Image caption Hisao Tanaka ya ce ya yi nadama

Shugaban kamfanin kera kayan lataroni mafi girma a Japan na Toshiba ya yi murabus daga kan mukaminsa, bayan da ya dauki alhakin wata babbar manakisar shigar da kudade da aka aikata.

Bayan da ya tsaya a gaban jama'a ya nuna nadamarsa, Hisao Tanaka ya shaida wa wani taron manema labarai cewa abin kunyar da aka aikata shi ne mafi illa da ya taba aukuwa a tarihin kampanin na Toshiba na shekaru 140.

Ya ce "Muna daukar abin da ya farun da muhimmancin gaske, kuma muna neman gafara. Akwai ma sauran manyan jami'an kampanin da su ma za su ajiye mukamansu."

Masu bincike sun gano cewa tun a shekarar 2008, kamfanin na Toshiba ya yi ta yin zulake na irin ribar da yake samu da dala biliyan daya da miliyan dari biyu.

Kuma manajoji kamfanin na sane da wannan dabi'a, saboda suna son cike wasu sharudda masu tsauri da aka gindaya masu.