Ana safarar yara 'yan kwallo zuwa Laos

Image caption Wani yaro dan wasan kwallon Afrika , shima yayi bayanin zaman sa a makarantar, inda ya ce an ajiye su tamkar bayi.

BBC ta samu labarin cewa ana safarar 'yan kawallon kafa masu shekaru kasa da 14 zuwa Laos, kuma ana tilasta masu sanya hannu a kwantiragin buga kwallo.

Bincike da BBC ta yi, ta gano wasu yara shida a kulob din Champasak United na Laos, bayan an shigo da kananan yara 23 daga Afrika ta gabas zuwa wata makarantar 'yan kwallo marar rajista a watan Fabrairu.

Dokar hukumar kwallon kafa watau Fifa dai ta hana shigar da yara wani kulob ko makarantar kwallo sai sun kai shekaru 18.

Kulob din da ke wani birni kusa da kudancin Pakse dai ya musanta wani zargin aikta ba daidai ba.

Wani kakakin hukumar ta Fifa ya shaida wa BBC cewa, "Fifa tana tuntubar kungiyoyi daban-daban domin samo bayanai akan lamarin saboda kare hakkokin yaran".

Ana zargin cewar sabuwar kungiyar ta Champasak United, da ke buga wasa a babbar gasar kwallo ta garin Laos, tana so ta ci riba ne wurin tallar 'yan wasa nan gaba.

Image caption Yaran sun shaidawa BBC cewar sun zauna a mawuyacin hali, inda dakin da suke ciki ma shi da ko taga.

A wani yunkuri da ya keta dokokin hukumar kwallon kafa ta duniya, kulob din ya fito da 'yan wasa 'yan kasa da shekaru 14 da 15 a gasar kwallon wannan shekarar.

Image caption Kwantiragin da Kamara ya sanya hannu ciki ta masa alkawarin biyansa albashi $200 duk wata.

Dan wasan kasar Liberia Kesselly Kamara, mai shekaru 14, wanda ya ci kwallo a wata gasa, ya ce an tilasta masa sanya hannu a kwantiragin shekaru shida kafin ya buga a ajin manya.

Kamara ya ce an masa alkawarin albashi da muhalli amma ba a cika ba domin a kasa ya ke kwana cikin filin wasan kungiyar kamar duk sauran 'yan tawagar tasu.

Image caption Alex Karmo yana kiran kansa "Shugaban 'yan wasan Afrika" a Laos.

Yaran da suka shiga makarantar ta "IDSEA Champasak Asia Africa Academy", sun samu gayyata ne daga tsohon kyeftin din kungiyar, Alex Karmo.

"Wannan makarantar ba a kafa ta bisa doka ba" In ji wani dan jarida kuma mai tallata wasanni a Liberia, Wleh Bedell, wanda ya jagoranci kungiyar zuwa Laos a watan Fabrairu.

Wleh Bedell ya ce, "makarantar bata da koci, babu kuma likita, shi Karmo shi ne ke shugabancin komai, duk shirme ne".

Takurar da wata kungiya, wadda ta hada hukumar Fifa da 'yan wasannin kasa da kasa, FIFPro, ta yi wa kulob din Champasak din ya sa aka saki yara 17, cikinsu kuma har da Kamara, amma kuma wasu yaran su shida sun zauna.

Iyayen matasan dai sun samu kan su cikin wani mawuyacin hali na bashi, tunda sun karbi kudade har dala 550, domin su biya kudin tafiya zuwa Laos, kuma har daya daga cikin zancen ma ya kai ga 'yan sanda Liberia.

Akwai dokokin Fifa da suka yarda da shigar da yara da basu kai shekara 18 ba cikin kwallon kafa, amma wannan yanayin ya bambanta kwarai da gaske.