Amurka ta ce zaben Burundi na da aibi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Daidaikun mutane ne suka fito kada kuri'a

Amurka ta ce zaben shugaban kasar da ake gudanarwa a Burundi yana da aibi sakamakon ce-ce-ku-cen da ake yi a kansa.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar, John Kirby, ya ce zaben zai kara rage wa gwamnatin kasar tagomashi.

Shugaba Pierre Nkurunziza dai na neman ta-zarcen wa'adin mulkin karo na uku, duk kuwa da cewa kundin tsarin mulkin Burundi ya takaita wa shugaban kasar wa'adin mulki sau biyu ne.

'Yan takara da dama daga bangaren jam'iyyun adawa sun kaurace wa zaben, yayin da 'yan kasar masu yawa ba su fita yin zabe ba.

Sai dai akwai dogayen layukan masu zabe a garin Buye, mahaifar Shugaba Nkurunziza, kuma shugaban, wanda ya je rumfar zabe a kan keke domin ya kada kuri'arsa.