An kashe Muhsin al-Fadhli jagoran Alka'ida

Image caption muhsin_al-fadhli

Amurka ta ce ta kashe wani babban jagora na kungiyar alka'ida a wani hari ta sama da ta kai Syria.

Wata sanarwa daga hukumar tsaron kasar ta ce an kaiwa Muhsin al-Fadhli harin ne a lokacin da yake cikin mota a kusa da garin Sarmada a ranar 8 ga watan da muke ciki.

An dai bayyana shi a matsayin jagoran kungiyar Khorasan wadda kungiyar alka'ida ta aiko su daga Pakistan zuwa Syria domin su kaddamar da hare-hare.

Ana dai zargin Al-Fadhli da hannu a cikin harin da aka kai kan tashar jiragen ruwan Amurka a Kuwait a shekarar 2002.

Gwamnatin Amurkan ta bayar da sanarwar bayar da ladan dala miliyan 7 ga duk wanda ya kawo rahoton kamashi ko kashe shi.