Bam ya tashi a Marwa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wannan shi ne karon farko da bam ke tashi a Marwa tun lokacin da Boko Haram ta sha alwashin kai hare-hare a Kamaru.

Rahotanni daga Kamaru na cewa wani abin da ake zaton bam ne ya fashe a garin Marwa da ke yankin Arewa mai nisa.

Babu dai wani karin bayani game da ko wasu sun jikkata.

Wannan shi ne karon farko da bam ke tashi a Marwa tun lokacin da Boko Haram ta sha alwashin kai hare-hare a Kamaru.

A baya dai kungiyar boko Haram ta sha kai hare-hare a kasar ta Kamaru da ma makwabtanta, wato Najeriya da Nijar da Chadi.

Kasashen suna hada gwiwa da zummar murkushe kungiyar, wacce ta kashe dubban mutane.