Za mu iya tattaunawa da Boko Haram — Buhari

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ba za ta kore yiwuwar tattaunawa da 'yan kungiyar Boko Haram ba dangane da sakin 'yan matan sakandare na Chibok sama da 200 da kungiyar ta yi garkuwa da su tun a watan Aprilun shekarar 2014.

Shugaba Buhari ya fadi hakan ne a yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin na CNN ranar Talata a kasar Amurka, a ci gaba da ziyarar kwanaki hudu da yake yi a kasar.

Sai dai kuma shugaban ya ce dole ne gwamnatinsa ta yi takatsantsan wajen sahihancin aniyar shugabannin kungiyar a kan tattaunawar.

Ya ce sai an tabbatar da su waye jagororinta na hakika domin mutane da dama suna fitowa su yi ikirarin jagorancin kungiyar.

Dangane kuma da batun yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Buharin ya ce babu wani mutum da zai zama shafaffe da mai domin kasancewarsa dan wata jam'iyya ko kuma yana jin shi wani ne.