Buhari ya koma Nigeria daga Amurka

Hakkin mallakar hoto Nigeria government
Image caption Buhari ya koma Najeriya daga Amurka da asubahin ranar Alhamis.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma Najeriya bayan ziyarar kwanaki hudu da ya kai kasar Amurka.

Shugaba Buhari ya koma kasar ne da asubahin ranar Alhamis, inda manyan jami'an gwamnati -- cikin su har da mataimakin shugaban kasa -- suka tarbe shi a filin jiragen saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja.

A lokacin da yake ziyarar, shugaban Najeriya ya gana da Shugaba Barack Obama, wanda ya yaba wa Shugaba Buhari, kana ya sha alwashin taimakawa Najeriya a yunkurin da take yi na murkushe kungiyar Boko Haram da kuma kwato kudaden da aka sace, aka boye a kasashen waje.

Baya ga Shugaba Obama, Shugaba Buhari ya gana da manyan jami'an gwamnatin Amurka da 'yan Najeriya mazauna Amurka, inda ya dauki alkawarin yin bakin kokarin sa wajen inganta rayuwar 'yan Najeriya.

Masana harkokin yau da kullum dai na ganin wannan ziyara za ta kara daukaka martabar Najeriya a idanun duniya, sannan ta kawo karshen zaman doya-da-manja da ake yi tsakanin Amurka da Najeriya sakamakon zargin take hakkin bil adama da Amurka ke yi wa sojin Najeriya.