'An gana wa wani yaro azaba har ya mutu a Kaduna'

Hakkin mallakar hoto kaduna govt

A jahar Kaduna da ke Najeriya, 'yan uwan wani yaro wanda aka ce wasu mutane sun ganawa azaba har ya mutu, na kokarin ganin sun kwatowa mamacin hakkokinsa.

Rahotanni dai na zargin cewa wani mai hali ne a wata Unguwa a Zaria, ya bayar da umarni a binciki yaron bayan da aka same shi da zargin satar wayar hannu.

Masu neman kadin wannan batu dai, sun ce tuni suka mika lamarin ga wata kungiya ta kare hakkin bil adama a Kaduna.

A Najeriya dai ana yawan samun masu yankewa mutanen da ake zargin sun aikata wani laifi hukunci, ba tare da an mika su ga hukumomin da suka dace ba.