An gano maciji mai kafa hudu

Hakkin mallakar hoto
Image caption Binciken ya nuna cewa micijin ya kwashe shekaru miliyan 113 a duniya.

Masana kimiyya sun gano maciji na farko a tarihi mai kafa hudu a cikin wasu dadaddun itatuwa a Brazil.

Wani bincike da aka wallafa a mujallar kimiyya ta Science ya nuna cewa micijin ya kwashe shekaru miliyan 113 a duniya.

Kazalika, bincike ya gano wasu macizan masu karfar-baya.

Daya daga cikin masu binciken, Dr Nick Longrich daga Jami'ar Bath ta Biritaniya ya ce binciken wani abin alfahari ne.