Obama: An tsaurara tsaro a Kenya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Obama ya ce ziyarar tasa tana nuna da irin dukufar da Amurka ta yi wajen yaki da ta'addanci a gabashin Afirka.

An tsaurara matakan tsaro a Nairobi, babban birnin kasar Kenya inda ake sa ran saukar shugaban Amurka Barack Obama nan da wasu 'yan sa'o'i.

An datse wasu manyan hanyoyi, tare da girke jami'an tsaro a cikin birnin, yayin da wasu jiragen saman Amurka ke ci gaba da shawagi a sararin samaniya.

'Yan kungiyar Al shabab dai sun sha kai hare-hare a cikin kasar ta Kenya.

Kenya dai ita ce kasar mahaifinsa ta asali, kuma ya shaida wa BBC cewa ziyarar tasa tana nuni da irin dukufar da Amurka ta yi wajen yaki da ta'addanci a gabashin Afirka, yana cewa Amurka za ta taka rawa wajen ganin cewa jarin da kasar China ke zubawa a Afirka ya amfani al'umar nahiyar.

Ya ce burinsa shi ne tabbatar da cewa kasuwancin ya amfani talakawan Kenya da na kasar Habasha ba wasu attajirai 'yan kalilan ba.