Obama ya jinjinawa 'yan kasuwar Kenya

Shugaba Obama da shugaba Uhuru Kenyatta.
Image caption Wannan ziyara da shugaba Obama ya kai Kasar kenya, ita ce ta farko da ya kai tun fara shugabancin Amurka.

Shugaban Amurka, Barak Obama ya yaba wa kasar Kenya dangane da yanda ta kasance ja-gaba a fagen kirkire da kuma kasuwanci a nahiyar afirka.

Ya yi wannan yabon ne lokacin bude wani taron kasa da kasa a kan harkokin kasuwanci a duniya. Shi ma takwaransa, wato shugaba Uhuru kenyatta na Kenya ya bayyana nahiyar Afirka da cewa tana cike da kafofin samun karuwa masu dimbin yawa, ya kamata a daina yi mata kallon kaskanci .

Mr Obama yace Afurka ta kama hanyar habaka da bunkasa, kuma kasar ta kasance a sahun gaba, ta na daya daga cikin nahiyoyin da ke saurin habaka a duniya.

Ana cire al'uma daga cikin talauci, kudin-shigar jama'a na karuwa. Kuma matasa na cin gajiyar fasahar zamani wajen sauya tsarin kasuwanci a Afurka.

Hakan alamun samar da wata muhimmiyar dama ga al'umomin Afurka da kuma duniya baki daya.