'Malamai ba sa iya caccakar Boko Haram'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar Boko Haram ta yi baranar kashe wasu malamai

A cikin wata kasida da ya gabatar game da maganar tsaro, Gwamna Kashim Shettima na jahar Borno ya furta cewa a yanzu haka babu shahararun malamai a arewacin kasar, da ke wayar da kawunan jama'a game da akidar 'yan kungiyar Boko Haram.

Kashim Shettima ya ce malaman addinin ba sa iya fitowa fili su na sukar akidojin 'yan kungiyar saboda fargabar abinda zai iya biyowa baya.

Don haka Gwamnan yai kira da a samarwa da malaman addinin kariya ta tsaro.

Gwamnan ya kara da cewa a wani karon, hatta 'yan jaridu ba sa gabatar da labarai, ta yadda za su taimakawa jami'an tsaro a cikin aikin su.