Mutane 16 sun rasu a Damaturu

Wani harin bam a jihar Yobe. Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ba wannan ne karon farko da birnin na Damaturu ke fuskantar hare-hare irin wannan ba.

Rahotanni daga Damuturu a jihar Yobe da ke arewacin Nigeria na cewa an samu harin kunar bakin wake a bakin kasuwar birnin da safiyar nan.

Harin ya faru ne a daidai lokacin da 'yan kasuwa ke fara gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

A kallah mutane 16 ne suka rasa rayukansu ya yin da wasu 46 suka jikkata, kuma tuni jami'an tsaro sun killace wurin tare da bukatar 'yan kasuwa da su rufe shagunansu saboda zaton da ake yi akwai wani bam din da aka dasa a kasuwar.

Babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin, amma ana danganta irin wadannan hare-hare da kungiyar Boko Haram wadda ke ikirarin kafa daular musulunci a arewacin Nigeria.

Wanann hari shi ne na 3 da aka kai birnin na Damaturu cikin kasa da mako biyu, kuma dukkan hare-haren na kunar bakin wake ne da aka kai babban masallacin Idi da safiyar Sallah karama.

Sai kuma wani harin na daban da wasu mutane suka kai a wurin binciken ababen hawa, akan babban titin Maiduguri zuwa Damaturu.

Ga kuma harin da aka kai na yau, dukkan hare-haren dai an rasa rayuka da dama, wasu kuma sun jikkata.