Kamaru: An kashe akalla mutane 19 a Maroua

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana zargin 'yan Boko Haram ne suke kai hari a Maroua

Mutane akalla 19 ne suka mutu bayan wani harin kunar bakin wake da aka kai a garin Maroua na arewacin Kamaru

Majiyoyin soji sunce harin ya auku ne a lardin Pont Vert a garin

Mutane da dama kuma sun jikkata a harin

Ko a ranar Laraba ma akalla mutane 20 ne suka mutu a wasu tagwayen hare- haren kunar bakin wake da aka kai a wata Kasuwa.

Jami'ai dai na zargin kungiyar Boko Haram ce ta kai harin