Obama ya kammala ziyara a Kenya

Shugaban Obama da Uhuru Kenyatta na kasar Kenya
Image caption Shugaban Obama da Uhuru Kenyatta na kasar Kenya

Shugaban Amurka Barak Obama ya kammala ziyarar da ya kai kasar Kenya, da yi wa 'yan kasar isharar cewa za su iya kyautata makomarsu.

Yana kuma mai gargadi a kan hadarin da ke tattare da matsalar cin-hanci da kuma kabilanci.

Don haka ya ja hankulan matasan kasar cewa ganin kwazon da suke da shi, su kara daura damara domin gina kasar.

Mr Obama, ya yi jawabi ne ga wani dandazon al'umar Kenya a wani dandalin wasanni a Nairobi, babban birnin kasar, inda ya ce Kenya na kan wani siradi, amma akwai haske a makomarta.

'Cin zarafin mata'

Mr Obama ya yi tur da batun da yace muguwar al'adar cin zarafin mata, da yiwa 'yaya mata kaciya da kuma auren dole, maimakon tura su makaranta-

Sai dai shugaba Obaman da takwaransa na kasar Kanyer Uhuru Kenyatta sun sha ban-ban ainin kan batun yancin 'yan luwadi.--yayinda Mr Obama ya yi kalaman adawa da nuna wariya ga 'yan luwadin , shi kuwa Mr Kenyatta bai nuna amincewarsa da batun ba.

Ziyayar ta shugaba Obama zuwa kasar ta Kenya , ita ce karon farko da ya ziyarci tushen mahaifinsa, tun bayan da ya zama shugaban kasa.

Nan gaba a yau ne dai zai wuce kasar Habasha, kuma zai kasance shugaban Amurka na farko da ke kai ziyara kasar, kana shugaban Amurka na farko da zai yi jawabi a taron kasashen membobin kungiyar Tarayyar Afirka a ranar Talata.