Shugaba Obama ya isa kasar Habasha

Shugaban Amurka Barack Obama
Image caption Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaba Obama ya isa kasar Habasha, bayan kammala ziyararsa a kasar Kenya, inda ya yi hasashen 'yan kasar za su iya gyara makomarsu.

Ya kuma yi gargadi a kan hadarin da ke tattare da matsalar cin-hanci da kabilanci a kasar ta Kenya.

Don haka ya ja hankulan matasan kasar cewa ganin kwazon da suke da shi, su kara daura damara domin gina kasar.

Mr Obama, ya yi jawabi ne ga wani dandazon al'umar Kenya a wani dandalin wasanni a Nairobi, babban birnin kasar, inda ya ce Kenya na kan wani siradi, amma akwai haske a makomarta.

Ziyayar ta shugaba Obama zuwa kasar ta Kenya , ita ce karon farko da ya ziyarci kasar da tushen mahaifinsa yake, tun bayan da ya zama shugaban kasa.

Yanzu haka Mr Obaman ya isa kasar Habasha, kuma ya kasance shugaban Amurka na farko da ya kai ziyara kasar.

Kana shugaban Amurka na farko da zai yi jawabi a taron kasashen membobin kungiyar Tarayyar Afirka a ranar Talata a kasar.