Obama zai kammala ziyara da jawabi a filin wasa

Shugaba Obama zai kammala ziyarar da yake yi a Kenya tare da wani jawabi ga dubban mutane a filin wasa dake babban birnin kasar Nairobi

Ana tsammanin zai tabo wuraren da Kasashen biyu suke da alaka ta fannin al'adu da kuma fata, sannnan zai tabo batun kare 'yancin dan- Adam

A ranar asabar Mr. Obama ya yaba da rawar da gwamnatin Kenyan ke takawa a yakin da ta ke yi da 'yan kungiyar al-shabab

Shugaba Obama ya kuma yi magana a kan mahimmancin kiyaye hakkin dan -Adam yayin yaki da ta'addanci da kuma kyakyawan shugabanci