Buhari ya nemi 'yan APC a majalisa su sasanta

Shugaba Muhammadu Buhari
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari

'Yan majalisar wakilan Najeriya sun shiga wata ganawa a cikin daren nan domin cimma matsayar karshe kan warware rikicin shugabancin da ake yi a Majalisar.

Wannan dai ya biyo ne bayan wata 'yar gajeruwar ganawar sirri da shugaban kasar ya yi ne da dukkan wakilan majalisar 'yan jam'iyyarsa ta APC dazu a fadarsa.

Shugaban ya bukaci 'yan majalisar da su kawo karshen rikicin ta hanyar yin biyayya ga jam'iyyarsu wadda ta kawo su majalisar.

Ranar Talata suke komawa zama a majaliar, bayan hutun da suka yi.