Buhari zai gana da 'yan majalisa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, zai gana da shugabanni da sauran 'ya'yan jam'iyya mai mulki ta APC na zauren majalisar wakilan kasar, a ranar Litinin.

Ganawar za ta zamo wani mataki na dinke barakar da ke tsakanin 'yan majalisar game da nade-naden shugabannin majalisar.

Al'amarin dai ya fara ne a lokacin da jam'iyyar APC ta aike wa kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara wasika mai kunshe da jerin mutanen da jam'iyyar take son a bai wa wasu mukamai.

Rashin bin umarnin jam'iyyar da kakakin majalisar, Yakubu Dogara ake zargin ya yi shi ne ummul-aba'isin wannan rigima.

Dogara dai ya ce ya ki bin umarnin jam'iyyar ne saboda batun yana kotu.

A karshen makon nan kuma wani bangaren da ke goyon bayan Femi Gbajabiamila, wanda jam'iyyar ta so a ba wa mukamin shugaban masu rinjaye a majalisar ta wakilai, ya ce an yi sulhu da bangaren Yakubu Dogara.

Sai dai wasu 'yan bangaren na Gbajabiamila sun karyata batun.

Ganawar da Buharin zai yi da 'yan majalisar tana zuwa ne kwana daya kafin majalisar ta koma bakin aiki bayan kwashe kimanin wata guda suna hutu.