An kai hari ofishin 'yan sanda a India

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan sandan India

Jami'an tsaro a kasar India sun kewaye ofishin 'yan sanda bayan wasu 'yan bindiga sun kai hari wajen wanda ke kusa da iyakar kasar da Pakistan.

'Yan sanda dai sun yi musayar wuta da 'yan bindigar a lokacin da su ka kai harin.

An kashe akalla mutane hudu a yayin arangamar inda daya daga cikin su dan sanda ne.

Mai magana da yawun 'yan sandan a kasar ya ce 'yan bindigar wadanda ke sanye da kakin sojoji sun kwace wata mota a safiyar yau a Punjab inda daga nan ne suka farwa wata tashar motoci a Gurdaspur kafin daga bisani su je ofishin 'yan sandan.

An dai gano bama-bamai 5 a kusa da wata tashar jirgin kasa.