Tandja Mamadou ya dawo gida Niger

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Tsohon shugaban Niger, Tandja Mamadou

Tsohon shugaban kasar Jamhuriyar Nijar, Malam Tandja Mamadu ya koma gida daga kasar Faransa inda ya yi jinya ta tsawon watanni.

Dimbin magoya bayansa ne dai suka kasance a filin jirgin sama na Diori Hamani da ke Yamai domin tarbensa, a jiya Lahadi.

A wani lokaci can baya dai har an furta cewa Allah ya yi masa cikawa, amma daga bisani aka gano cewa labarin na cike da kuskure.

Firaiministan kasar, Birji Rafini ne dai ya sanar da rasuwar tsohon shugaban kasar, Tandja Mamadu, a baya.

Wannan batun dai ya janyo kace-nace a tsakanin 'yan siyasar kasar a inda magoya bayan Tanda Mamadun suke ganin cewa jam'iyya mai mulki tana farin ciki da rashin lafiyar tshohon shugaban kasar ta Niger.