Turkiyya ba za ta aika sojoji Syria ba

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ahmet Davutoglu

Firai ministan Turkiyya, Ahmet Davutoglu ya ce kasarsa ba ta da niyyar aika sojojin kasa zuwa Syria domin yaki da 'yan kungiyar IS.

Mista Davutoglu ya kara da cewa harin da kasar ta kaddamar a kan 'yan kungiyar IS wani yunkuri ne na kare iyakokin kasar.

Ya ce jiragen Turkiyya da na Amurka za su iya tabbatar da tsare iyakokin kasar daga hare-haren masu tada kayar baya.

Mista Davutoglu ya kara da cewa kasar ta Turkiyya ta na kokarin ganin ta yi aiki tare da 'yan kabilar Kurdawa na kasar Syria idan ba za su zamo barazana ga kasar ba.

Sai dai kuma ya ce idan har suka kasance barazanar ga Turkiyyar, za su yabawa aya zakinta kana su kuma fuskanci bacin ran kasar kwatankwacin irin wanda 'yan awaren PKK suke fuskanta.