Boko Haram ta kai hari a kudancin Borno

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun Nigeria sun ce za su kawar da Boko Haram

Rahotannin daga jihar Borno sun ce mayakan Boko Haram sun kai wa wasu kauyuka da ke karamar hukumar Askira Uba a kudancin jihar hari.

Lamarin ya janyo mutuwar mutane da dama da kuma kona gidajen kauyukan.

Kauyen Dille na daga cikin kauyukan da aka kai harin.

Hon Jibrin Satumari dan majalisar jihar Borno ne mai wakiltar yankin na Askira Uba ya tabbatarwa BBC cewar al'ummomin kauyukan son boye a cikin duwatsu domin neman tsira.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar dubban mutane a yankin arewa maso gabashin Nigeria.