Sojoji sun kubutar da mutane 30 a Dikwa

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption 'Yan Boko Haram sun yi garkuwa da mutane da dama

Rundunar sojin Nigeria ta ce ta kubutar da mutane kusan 30 daga hannun 'yan Boko Haram a kauyuka biyu na Dikwa a jihar Borno.

Kakakin runduna ta bakwai na sojin Nigeria da ke Maiduguri, Kanar Tukur Gusau ya ce wadanda aka ceto din daga kauyukan Kwayabe da Wufe, sun hada da yara kanana 21 da kuma jariri dan watanni shida da mata bakwai da kuma tsofaffi biyu maza.

Rundunar ta ce ta kuma kwace makamai da dama na 'yan Boko Haram din wadanda suka kafa sansani a fadar Shehun Dikwa kafin sojojin su afka wurin.

Kanar Gusau ya kara da cewar sun gano wuraren horo na 'yan Boko Haram a lokacin da suka isa Dikwa din.

'Yan Boko Haram sun sace daruruwa mutane musamman mata a kauyuka da dama na jihar Borno.