An kori wasu jami'an gwamnatin Malaysia

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana zargin Mr Najib da satar kudin kasar.

Firai Ministan Malaysia, Najib Razak, ya kori mataimakinsa da Antoni-Janar bayan da suka zarge shi da cin hanci da rashawa.

An kori mataimakin Firai Ministan ne bayan ya fito bainar jama'a ya bukaci Mr Najib ya yi cikakken bayani a kan yadda ya tafiyar da wasu kudade daga asusun zuba jari.

A farkon watan nan, jaridar Wall Street Journal ta yi zargin cewa an kwashe kusan $700m daga asusun, sannan aka sanya su a asusun Firai Minista Najib na kashin kansa.

Antoni-Janar ne dai ke gudanar da bincike a kan batun.

Mr Najib ya musanta zargin da ake yi masa.