Obama ya soki tsarin tazarce a Afrika

Hakkin mallakar hoto
Image caption Obama ya ce akwai bukatar shugabannin Afrika su mutunta tsarin mulki

Shugaba Obama ya shaida wa shugabannin Afrika cewa ci gaban nahiyar ya ta'allaka ne a kan tsarin dimokradiyya, da ba da 'yancin walwala da kare hakkin bil'adama.

A jawabin farko da wani shugaban Amurka da ke kan kujerar mulki ya gabatar a zauren taron kungiyar Tarayyar Afrika, a birnin Addis Ababa na Habasha, ya ce ba yadda za a yi Afrika ta ci gaba matukar shugabanninta na kin sauka daga kan mulki a karshen wa'adin mulkinsu.

Obama ya ce matukar ana ci gaba da daure 'yan jaridu ana barazana ga masu fafutukar kare hakkin jama'a, to dimokradiyyar za ta kasance a fatar baki ne kawai.

Ya kuma yi gargadin cewa cin hanci da rashawa na janyo nakasu ga nahiyar, a maimakon a gina makarantu da asibitoci da kudaden.

Wasu shugabannin Afrika sun shafe shekaru da dama a kan mulki sun ka ba da dama a wani sabon zabe domin wasu su maye gurbinsu.