Takaddamar majalisar wakilai ta zo karshe

Image caption Shugabannin majalisun Najeriya

Alamu na nuna cewa an tasamma kawo karshen takaddamar da ake fuskanta kan batun shugabancin da ya dabaibaye 'yan jam'iyyar APC mai mulki a Majalisar dattawa da kuma Majalisar wakilai a Najeriya.

A yanzu haka dai 'yan Majalisar wakilan sun amince da Hon. Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban masu rinjaye a majalisar.

A bangare guda kuma, 'yan Majalisar dattawan kasar su 81 daga cikin 109 sun zartar da wani kudiri na amincewa da jagorancin shugaban Majalisar Sanata Bukola Saraki, da mataimakinsa Sanata Ike Ekweremadu da kuma sauran shugabannin Majalisar.

'Yan Majalisar Dattawan sun kuma bukaci rundunar 'yan sandan kasar da sauran jami'an tsaro da kada su bari wani ko wasu su rika amfani da su wajen muzgunawa ko cin zarafin daukacin 'yan Majalisar tare da iyalan su.

Rikicin dai ya samo asali ne a lokacin da jam'iyyar APC ta aike wa kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara wasika mai kunshe da jerin mutanen da jam'iyyar take son a bai wa wasu mukamai.