Ana shirin kai gawar Ooni na Ife Nigeria

Hakkin mallakar hoto wiki
Image caption Ooni na Ife babban Basaraken gargajiya ne a Najeriya.

Wata majiya ta shaida wa BBC cewar iyalan Ooni na Ife, wanda ya mutu a wani asibi a birnin London, suna can suna shirye shiryen yadda za su kawo gawar Oonin zuwa Najeriya.

Majiyar ta ce Oonin na Ife ya rasu ne a asibitin da ake kira London Clinic da ke tsakiyar birnin London.

A ranar Laraba ne dai kafafe sada zumunta da muhawara a Najeriya suka cika da labarin cewa Babban Basaraken gargajiyar na kasar yarabawa, Oba Okunade Sijiwade, ya rasu ranar Talata.

Lamarin dai ya sa daruruwan mutane sun yi wa fadarsa tsinke domin ganin halin da ake ciki.

Sai dai manyan jami'an fadar Basaraken sun fitar da sanarwar da ke cewa Oba Sijiwade bai mutu ba, suna masu cewa "yana cikin koshin lafiya kuma yana ta shirye-shiryen daurin auren daya daga cikin 'ya'yansa".

A al'adance dai, ba a sanar da mutuwar duk mutumin da ke rike da mukamin Oonin na Ife sai bayan wasu kwanaki, lamarin da wasu ke gani shi ne dalilin da ya sa fadarsa taki bayar da sanarwar rasuwar tasa".

Basaraken dai ya kwashe shekaru 35 a kan karagar mulki bayan hawa kan kujerar ta Oni a shekarar 1980.

Marigayi Oba Okunade ya kasance na hannun damar tsohon sarkin Kano, marigayi Alhaji Ado Bayero.