Sojoji sun ceto fararen hula 59 daga BH

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Daga cikin wadanda aka kubutar wasu cikin yunwa

Rundunar sojin Najeria ta ce ta ceto karin fararen hula 59 wadanda 'yan Boko Haram suka kama a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

Rundunar ta kuma fitar da sabbin hotuna da ke nuna yadda dakarunta ke gwagwarmaya a fagen daga a yakin da suke yi don murkushe mayakan Boko Haram.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Kanal Kukasheka Usman, ya fitar ta ce a wani sabon hai da aka kai wa mayakan Boko Haram an lalata sansanoninsu da ke Chogori da Shantumari a jihar Borno.

A yayin da aka kai wasu hare-haren a kan masu tayar da kayar bayan da sun ta fitowa daga ramuka suna tserewa.

Kazalika, dakarun bataliya ta 151 ta rundunar hadin gwiwa sun kaddamar da wasu hare-haren a sansanonin masu tayar da kayan bayan Kashingeri da Wale da kuma Kushingari a ranar Alhamis.

A yayin hare-haren dai an kashe masu tayar da kayan bayan da dama.

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Dattawa na daga cikin wadanda aka ceto daga hannun 'yan Boko Haram