'Zan mutunta yarjejeniya a kan Bakassi'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta mutunta yarjejeniyar da ta mika tsibirin Bakassi ga Kamaru.

Buhari ya fadi hakan ne a lokacin da yake ganawa da 'yan Najeriya mazauna Kamaru, yayin ziyarar kwanaki biyu da ya kai kasar.

A shekarar 2002 ne dai kotun kasa-da-kasa ta yanke hukuncin mika tsibirin ga jamhuriyar ta Kamaru, bayan tsawon lokacin da kasashen biyu suka kwashe suna zaman tankiya a kan wanda ya kamata ya mallaki tsibirin mai albarkatun man fetir.

Dangane kuma da batun 'yan Najeriyar masu neman mafaka a Kamarun sakamakon hare-haren Boko Haram, Shugaba Buhari ya ce gwamnati tana yi musu shiri na musamman domin ganin an dawo da su zuwa garuruwansu na asali.

A ranar Alhamis din nan ne kuma Muhammadu Buhari yake kammala ziyarar aikin kwanaki biyu daya kai Jamhuriyar ta Kamaru.

Kasashen Kamaru da Najeriya na neman sabunta dangantakarsu a fannin tsaro, domin su yaki kungiyar Boko Haram.