Likitocin Ghana sun fara yajin aiki

Image caption Likitocin Ghana sun fara yajin aiki.

Likitoci a Ghana sun fara yajin aiki bayan rashin daidaituwa da suka samu da gwamnati kasar a kan inganta yanayin aikinsu.

Likitocin na korafin cewa bayan kudin dakin ajiye gawarwaki da ake sauwaka wa masu, babu wani tsari da aka gudanar na yanayin aiki ko yadda za su amfana, ko kuma nauyin da za su dauka.

Gwamnatin kasar dai ta ce ya kamata likitocin su bai ta lokaci domin tattaunawa a kan korafe-korafen nasu, da kuma yadda za su shigar da shi cikin tsarin kasafin kudin kasar.

Yajin aikin zai kawo babbar matsala ga gwamnatin Ghana wacce a haka ma take fama da matsalolin wuraren kiwon lafiya.