An rataye Yakub Memon a Indiya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yakub Memon

An zartar da hukuncin kisa a kan Yakub Memon, mutumin da aka samu da laifin daukar nauyin munanan hare-haren da aka kai a Mumbai a shekarar 1993.

An rataye shi a birnin Nagpur duk da cewa ya bukaci a yi masa sassauci a kan hukuncin, lamarin da kotun koli da kuma shugaban kasar ta Indiya suka yi watsi da shi.

Yakub Memon shi ne mutum na farko da aka zartar wa hukuncin kisa.

Hare-haren da aka kai a shekarar 1993 sun yi sanadiyyar rasa rayukan mutane 257.

Yakub Memon dai ya bar kasar Indiya tare da iyalansa kafin a kai hare-haren, bayan shekara guda kuma ya koma kasar.