Sanatoci za su ziyarci arewa maso gabas

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki

Majalisar dattawan Najeriya ta zartar da wani kudirin doka na tura tawaga ta musamman yankin arewa maso gabashin kasar.

Ana sa ran 'yan tawagar -- karkashin jagorancin shugaban majalisar dattawan Sanata Bukola Saraki -- za su ziyarci yankin ne domin su ganewa idanuwansu halin da yake ciki.

Abubuwan da za su duba dai sun hada da irin girman barnar da hare-haren Boko Haram suka yi wa yankin da yanayin da al'ummar yankin ke ciki sannan su saurari koke-kokensu.

Tawagar za ta kuma mayar da hankali a kan yanayi da halin da jami'an tsaro suke ciki a yankin.

Kazalika, Majalisar ta dattawa ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari da ya kafa kwamitin da zai yi aikin farfado da yankin da kuma sake dawo da mutanen yankin na arewa maso gabashin Najeriya gidajensu.