Chadi ta kashe 'yan Boko Haram 100

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Boko Haram sun fadada kai hare-harensu zuwa wasu kasashen da ke yankin tafkin Chadi

Rundunar sojin Chadi ta ce ta kashe fiye da mayakan Boko Haram 100 cikin makonni biyu da suka gabata a wani gumurzu da ake yi a tafkin Chadi da kewaye.

Babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin.

Kungiyar Boko Haram ta fara kai hare-harenta ne a Najeriya amma yanzu ta kutsa wasu kasashen da ke yankin.

A ranar Alhamis ne majalisar dokokin Chadi ta kada kuri'ar mai do da hukuncin kisa a kan 'yan ta'adda, bayan da aka soke hukuncin watanni shida da suka gabata.

'Yan adawa da kuma kungiyoyin fararen hula sun soki dokar yaki da ta'addancin, suna masu cewa za a yi amfani da ita ne wajen tauye 'yancin fararen hula.