Obama ya umarci a kirkiro kwamfuta mafi sauri

Hakkin mallakar hoto White House
Image caption Obama ya bukaci masana kimiyya su kirkiro da kwamfuta mafi sauri a duniya

Shugaba Obama ya yi kira ga Amurka da ta kirkiri na'urar kwamfutar da ta fi kowacce sauri zuwa shekarar 2025

Kwamfitar da ake son a kirkiro zata nunka wacce ake amfani da ita a yanzu 'yar China sauri wajen gudanar da aiki har sau ashirin

Kwamfutar za ta iya lissafin biliyoyi cikin dakika daya

Za a kirkiro da wani shiri na NSCI domin gudanar da bincike sannan kuma da kera kwamfutar

Amurka na bukatar irin wannan kwamfuta mai sauri domin gudanar da ayyuka da suka hada da binciken kimiyya da kuma manyan ayyukan da suke shafi tsaron kasa

Ana fatan cewa na'urar za ta taimaka wajen duba bayanan yanayi ko kuma taimakawa wajen gano cutar daji bayan an dauki hoton jikin dan-adam