Wata mata ta tsira daga bakin wani Kada a India

Kada
Image caption Kada

A kasar India wata mata a wani kauye dake jihar Orissa ta kubuta daga bakin wani gawurtaccen Kada da ya yi yunkurin hallaka ta.

Matar mai suna Sabitri Samal ta bayyana yadda ta tsallake rijiya da bayan da cewa, Kadan mai tsawon mita uku ya cafke ta ne a lokacin da take wanke-wanke a bakin kogi.

Ta ce ta yanke kauna daga kubuta daga bakin Kadan a lokacin da ya janye ta cikin kogin.

Amma kuma a fafatawarsu da shi ne ta kai masa naushi a ka-- inda cikin fusata sai Kadan sannu a hankali ta sake ta.

Yanzu haka ana yi mata magani a wani asibiti sakamakon raunukan da ta samu.

Rahotanni sun ce a baya bayan nan Kadoji sun hallaka mutane biyu tare da jikkata bakwai a wannna yanki dake kusa da wani gandun daji.