An kama babban Kwamandan Boko Haram

Hakkin mallakar hoto nigeria defence forces
Image caption Sojojin Nigeria na ci gaba da fafatawa da 'yan Boko Haram

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar tarwatsa sansanoni takwas na 'yan ta'adda a wani farmaki da suka kaddamar ranar Lahadi .

Rundunar ta ce an kuma sami nasarar cafke wani babban Kwamandan mayakan Boko Haram da ransa, kuma yanzu haka za a yi masa tambayoyi.

Sojojin sun ce sun kuma sami nasarar kubutar da mutane 178 daga 'yan ta'addan ,da suka hada da kananan yara da mata da kuma maza .

To sai dai wannan nasara da sojojin suke cewa sun samu, na zuwa ne daidai lokacin da mayakan Boko Haram din suka fitar da wani bidiyo a jiya Lahadi, inda suke ikirarin samun nasara a kan sojojin.

Sai dai mai magana da yawun rundunar sojin Nigeriar Kanal Sani Kukasheka Usman ya yi watsi da ikirarin nasu inda ya ce 'wannan maganar ba ta da tushe balle makama'.