An hallaka na hannun damar Nkurunziza

Shugaba Pierre Nkurunziza Hakkin mallakar hoto
Image caption Kasar Burundi ta shiga rikita-rikitar siyasa dun a watan Afrilun da ya gabata.

Wasu mahara sun hallaka Ganal Adolphe Nshimirimana, a kusa da babban birnin kasar Bujumbura.

Jami'in yada labaran fadar Burundi Willy Nyamitwe ne ya sanar da 'yan jarida batun mutuwar ta sa ba tare da yin wani karin bayani ba.

Kuma tuni jami'an tsaro suka killace hanyar da aka kai harin, tare da hana ababen hawa da mutane zirga-zirga a yankin. An kuma ci gaba da jin karar harbin bindiga babu kakkautawa a wajen da safiyar nan.

Babu dai wani mataki da hukumomin kasar suka dauka, sai da Mr Nyamitwe ya wallafa a shafinsa na twitter cewa 'ya rasa dan uwansa mai kishin al'uma.

Wannan mutuwa ta Ganal Nsimirimana bababn koma baya ce ga shugaba Pierre Nkurunziza.

Dan an tabbatar da cewa Ganal din na hannun daman shugaba Nkurunziza ne, duk kuwa da cewar a watan Nuwambar shekarar da ta wuce a sauke shi daga mukamin babban jami'in hukumar leken asirin kasar,amma an ci gaba da kallonsa a matsayin wani mai fada a ji a kasar ta Burundi.