'Yan Sandan Brazil na kashe jama'a'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A badi ne ake saran gudanar da wasannin guje guje da tsale tsalle a Brazil

Kungiyar kare hakkin dan-Adam ta Amnesty International tace 'yan sandan a birnin Rio de Janeiro a kasar Brazil su ne ke da alhakin mutuwar mutane fiye da 1,500 a shekaru biyar din da suka gabata

Kungiyar ta ce ta gano hujjar dake nuna cewa a wata unguwar talakawa dake arewacin birnin ta Acari, Tara daga cikin irin wadannan kashe- kashen da aka yi guda 10, an yi su ne ba bisa- doka ba.

Ta ce a yawancin lokuta, wadanda ake kashewa sun mika kansu ko kuma an ji musu ciwo a lokacin da jami'an 'yan sanda suka kashe su.

Rahotan Amnesty wanda aka wallafa gabanin wasannin Olimpics da za'a yi a Rio a badi, ya kuma ce ba kasafai ake gudanar da binciken irin wadannan abubuwa dake faruwa ba tare da hukunta wadanda suke aikata kisan

'Yan sandan Brazil ba suce komai ba, game da wannan rahoto ya zuwa yanzu